‘Yan sanda a Adamawa sun kafa sabuwar rundunar yaƙi da manyan laifuka

0
‘Yan sanda a Adamawa sun kafa sabuwar rundunar yaƙi da manyan laifuka

‘Yan sanda a Adamawa sun kafa sabuwar rundunar yaƙi da manyan laifuka

Spread the love

Hukumar ‘yan sanda ta Jihar Adamawa ta sanar da rushe tsoffin rundunonin musamman tare da kafa sabuwar runduna mai suna Violent Crime Response Unit (VCRU) domin inganta yaki da manyan laifuka a jihar.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Kabir Umar Hassan, ne ya amince da kafa rundunar tare da naɗa Clarence Lawrence a matsayin kwamandan ta.

Wannan mataki na zuwa ne bisa umarnin Sufeto Janar na ‘yan sanda, Olatunji Rilwan Disu, domin daidaita ayyukan rundunonin musamman zuwa tsari guda.

Kafin wannan sauyi, rundunar ‘yan sanda a jihar na da rundunoni biyar na musamman, amma yanzu an rushe hudu daga ciki, inda aka tura jami’ansu zuwa sassan ‘yan sanda daban-daban.

Wasu daga cikin jami’an kuma za su samu horo na musamman kan kare hakkin dan Adam, ƙwarewar aiki da kuma sabbin dabarun aikin ‘yan sanda kafin a tura su sabuwar rundunar.

Sabon kwamandan rundunar, CSP Clarence Lawrence, ya shiga aikin ‘yan sanda tun shekarar 2009, kuma ya yi aiki a wurare daban-daban a fadin ƙasar nan. Haka kuma ya halarci horo da dama a ciki da wajen ƙasa, wanda ya ƙara masa ƙwarewa wajen gudanar da aiki.

Yayin da yake miƙa masa wannan muƙami, kwamishinan ‘yan sanda ya umarce shi da ya tabbatar da aiki bisa ƙa’idoji, nuna ƙwarewa da kuma gaggauta amsa kiran gaggawa daga jama’a domin inganta tsaro a fadin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *