Ƴan Najeriya a Philippines da Cambodia sun bai wa Gwamnatin Najeriya wa’adin kwana bakwai kan harajin Diaspora

0
Ƴan Najeriya a Philippines da Cambodia sun bai wa Gwamnatin Najeriya wa’adin kwana bakwai kan harajin Diaspora

Ƴan Najeriya a Philippines da Cambodia sun bai wa Gwamnatin Najeriya wa’adin kwana bakwai kan harajin Diaspora

Spread the love

Wasu ƴan Najeriya da ke zaune a ƙasashen Philippines da Cambodia sun bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki bakwai da ta janye wata doka da ake zargin Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Manila ya kafa, wadda ta tilasta musu yin rajista da ƙungiyar NIDOPHIL tare da biyan kuɗaɗen membobinta kafin su samu ayyukan ofishin jakadanci.

Rahotanni sun bayyana cewa ofishin jakadancin ya sanar da cewa babu wani ɗan Najeriya da za a yi wa hidimar ofishin jakadanci sai ya gabatar da shaidar rajista da NIDOPHIL, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin mazauna ƙasashen biyu. Haka kuma an ce dokar ta shafi ɗaliban Najeriya da ke karatu a Philippines.

Lauyoyin da ke wakiltar waɗannan ƴan Najeriya ƙarƙashin jagorancin Chukwuma Nwachukwu sun aika da ƙorafi ga Ministar Harkokin Wajen Najeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, inda suka bayyana matakin a matsayin take haƙƙin ɗan adam da kuma saɓawa kundin tsarin mulkin ƙasa da ya bai wa kowa damar shiga ko ƙin shiga kowace ƙungiya.

Masu ƙorafin sun ce babu wata doka da ta bai wa ofishin jakadanci ikon tilasta wa ƴan Najeriya shiga NIDOPHIL kafin samun ayyukan da suka haɗa da sabunta fasfo, takardun karatu da sauran hidimomin ofis.

Sun kuma yi gargadin cewa matakin na iya jefa ɗalibai da sauran mazauna ƙasashen cikin matsala mai tsanani.

Sun bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta janye sanarwar cikin kwanaki bakwai, tare da yin barazanar garzayawa kotu idan ba a dauki mataki ba.

A cewarsu, duk wani ɗan Najeriya mai ingantaccen fasfo yana da cikakken haƙƙin samun ayyukan jakadancin ƙasarsa ba tare da wani sharadi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *