Zaɓen 2027: Masana sun gargadi APC kan illar ci gaba da tsare Nasir El-Rufai
El-Rufai ya isa kotu a Kaduna domin ci gaba da shari’arsa
Ci gaba da tsare tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya haifar da muhawara kan tasirinsa ga siyasar Najeriya yayin da ake tunkarar babban zaben 2027.
Wasu masana siyasa sun bayyana cewa tsare shi na dogon lokaci na iya shafar jam’iyyar APC, musamman idan jama’a suka fara kallon lamarin a matsayin batun siyasa maimakon shari’a.
Daraktan SEDSAC, da wasu manazarta da Daily Post ta tuntuba, sun ce ci gaba da tsare El-Rufai na iya janyo masa tausayi daga wasu ‘yan Najeriya, tare da kara masa karfin siyasa a idon magoya bayan adawa.
Sun ce lamarin na iya zama wata dama ga masu adawa da gwamnati wajen gabatar da shi a matsayin wanda ake gallaza wa saboda bambancin ra’ayin siyasa.
Sai dai hukumomin yaki da cin hanci da rashawa sun sha nanata cewa ana gudanar da binciken El-Rufai ne bisa tanadin doka da umarnin kotu, yayin da ake zarginsa da wasu laifuka da suka shafi mulkinsa a Kaduna.
A gefe guda, wasu ‘yan adawa sun dade suna zargin cewa tsare shi na da alaka da siyasar 2027, zargin da hukumomin gwamnati suka musanta.
Masu sharhi sun ce yayin da zaben 2027 ke kara karatowa, yadda gwamnati da hukumomin shari’a za su tafiyar da lamarin El-Rufai zai ci gaba da janyo hankalin jama’a.
Sun jaddada muhimmancin tabbatar da cewa shari’ar ta kasance cikin adalci da bin doka, domin kauce wa duk wani tunanin cewa ana amfani da hukumomin gwamnati wajen takaita harkokin siyasa.
