Galadima ya tallafa da N10m ga shirin ci gaban Nunguraya na Shekaru 20
Galadima ya tallafa da N10m ga shirin ci gaban Nunguraya na Shekaru 20
Tawagar dan takarar gwamnan jihar Adamawa na jam’iyyar APC, Ahmed Tijjani Galadima, karkashin jagorancin Darakta-Janar na Kungiyar Kamfen din Galadima/Kamale, Ambasada Kevin Peter, ta halarci bikin al’adun gargajiya na shekara-shekara na Nunguraya SINMILALAMA da kuma kaddamar da shirin raya yankin na shekaru 20 a Dishon Dansanda II Square, karamar hukumar Guyuk.
Tawagar, wadda ta kunshi Sakataren APC na jihar Adamawa, Mustapha Atiku Ribadu, Daraktan Kungiyoyin Tallafi, John Hamman, Hon. Aminu Bobboi Talban Zing, Hon. Dahiru Hamman Dikko da sauran mambobin kungiyar kamfen din Galadima/Kamale, ta isar da sakon gaisuwar Ahmed Tijjani Galadima ga al’ummar Guyuk, tare da gode wa Kwandi Nunguraya bisa gayyatar da aka yi musu zuwa wajen taron.
Da yake jawabi a madadin Galadima, Ambasada Kevin Peter ya yaba wa al’ummar Nunguraya bisa tsara shirin raya yankin na shekaru 20, yana mai bayyana shirin a matsayin wani gagarumin yunkuri na dogon lokaci da ya kamata a yaba masa.
Ya kuma sanar da bayar da tallafin Naira miliyan 10 daga Tijjani Galadima domin taimakawa wajen aiwatar da shirin ci gaban al’ummar.
Ambasada Kevin Peter ya kuma tabbatar wa al’ummar Nunguraya cewa idan aka ba Ahmed Tijjani Galadima damar jagorantar jihar, zai ci gaba da tallafa wa shirin tare da yin kokarin ganin an cimma manufofinsa, domin bunkasa Nunguraya da kuma taimakawa wajen sauya fasalin karamar hukumar Guyuk baki daya.
Taron ya samu halartar sarakunan gargajiya, dattawa, al’umma, ‘yan siyasa da sauran manyan baki domin bikin al’adun Nunguraya da kaddamar da manufofin ci gabanta na dogon lokaci.
