’Yan ta’adda na amfani da Social Media da kuɗaɗen Kirifto wajen tallafa wa ta’addanci – Ribadu

0
’Yan ta’adda na amfani da Social Media da kuɗaɗen Kirifto wajen tallafa wa ta'addanci - Ribadu

’Yan ta’adda na amfani da Social Media da kuɗaɗen Kirifto wajen tallafa wa ta'addanci - Ribadu

Spread the love

Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, da Tarayyar Afirka (AU) sun yi gargaɗi kan yadda ’yan ta’adda ke amfani da kafafen sada zumunta da kuɗaɗen kirifto wajen ɗaukar sabbin mambobi da tara kuɗaɗen gudanar da hare-hare.

Sun yi wannan kiran ne a Abuja ranar Talata a wani taron horo na kwanaki uku na yanki kan gano da kuma dakile yadda ‘yan ta’adda ke amfani da fasahar sadarwa da bayanai da fasahohin zamani.

Sun bayyana cewa ƙungiyoyin ta’addanci na amfani da fasahar zamani wajen yaɗa farfagandarsu, jan hankalin matasa da kuma samar da kuɗaɗen tallafa wa ayyukansu, lamarin da ke ƙara ƙalubalantar ƙoƙarin hukumomin tsaro na yaƙi da ta’addanci.

Ribadu da AU sun jaddada muhimmancin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen Afirka, musayar bayanan sirri da kuma sa ido kan hanyoyin da ake amfani da su wajen samar da kuɗaɗen ta’addanci domin dakile ayyukan ƙungiyoyin.

Sun kuma yi kira da a ƙara amfani da dabarun zamani wajen gano tare da katse hanyoyin sadarwa da kuɗaɗen ’yan ta’adda, domin hana su ɗaukar mambobi, samun tallafin kuɗi da kuma kai hare-hare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *