Rashin tsaro ya sa sanatan Sakkwato ficewa daga APC

0
Rashin tsaro ya sa sanatan Sakkwato ficewa daga APC

Senator Ibrahim Lamido, Sokoto East.

Spread the love

Sanatan yankin gabashin Sokoto, Ibrahim Lamido, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC, yana mai danganta hakan da tsananin rashin tsaro da hare-haren ‘yan bindiga a yankinsa.

Ya ce hare-haren sun lalata ƙauyuka da dama tare da tilasta wa jama’a gudun hijira, yana mai zargin cewa matakan gwamnati ba su wadatar ba wajen magance matsalar.

Lamido ya bayyana cewa matakin nasa ya biyo bayan shawara da jama’arsa suka bayar, domin neman wata jam’iyya da za ta fi mayar da hankali kan tsaro da ci gaban al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *