Pantami ya yi martani bayan INEC ta cire sunansa daga jerin ’yan takarar gwamnan Gombe

0
Pantami ya yi martani bayan INEC ta cire sunansa daga jerin ’yan takarar gwamnan Gombe

Pantami ya yi barazanar tona asirin masu koƙarin hana shi zama Gwamnan Gombe

Spread the love

Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Farfesa Isa Ali Pantami, ya mayar da martani bayan Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar da jerin sunayen ’yan takarar gwamnan Jihar Gombe na zaɓen 2027 ba tare da sunansa ba.

Hukumar ta fitar da sunayen ’yan takara 16 da za su fafata a zaɓen gwamnan jihar da aka tsara gudanarwa a ranar 6 ga Fabrairu, 2027.

Pantami, wanda ya sauya sheƙa daga jam’iyyar APC zuwa PDP a ranar 19 ga Mayun 2026, ya sake lashe zaɓen fidda gwani na PDP bayan wata kotu ta soke zaɓen fidda gwani na farko tare da umartar jam’iyyar da ta sake gudanar da shi.

A martanin da ƙungiyar Pantamiyya Movement da shugabannin PDP a jihar suka fitar, sun danganta cire sunansa da wasu abokan hamayyar siyasa da suke ƙoƙarin kawo cikas ga burinsu na siyasa.

Sun kuma buƙaci magoya bayansa da su kwantar da hankulansu, su ci gaba da jajircewa da tallafa wa tafiyar siyasar Pantami.

Sai dai har yanzu ba a bayyana dalilin da ya sa INEC ta cire sunan Pantami daga jerin ba. Lamarin ya haifar da tambayoyi kan makomar takararsa da wakilcin PDP a zaɓen gwamnan Gombe na 2027, yayin da ake jiran ƙarin bayani daga hukumar zaɓe da jam’iyyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *