Pantami ya yi gargaɗin cewa ba wanda zai iya sauya sakamakon zaɓe a Gombe

0
Pantami ya yi gargaɗin cewa ba wanda zai iya sauya sakamakon zaɓe a Gombe

Pantami ya yi gargaɗin cewa ba wanda zai iya sauya sakamakon zaɓe a Gombe

Spread the love

Ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe na jam’iyyar PDP, Farfesa Isa Ali Pantami, ya bayyana cewa babu wanda zai iya sauya sakamakon zaɓen jihar, yana mai jaddada cewa al’ummar Gombe ne za su zaɓi shugabanninsu kuma kuri’unsu za su ƙidayu.

Pantami ya yi wannan furuci ne yayin ganawa da magoya bayan jam’iyyar PDP a ƙaramar hukumar Nafada da wasu sassan jihar, inda ya buƙaci gwamnatin jihar da hukumomin da abin ya shafa su tabbatar da adalci da gaskiya a lokacin zaɓen 2027.

Ya kuma ce jam’iyyarsa za ta gudanar da yaƙin neman zaɓe ne bisa gabatar da manufofi da shirye-shiryen ci gaba, ba tare da cin zarafi ko tada husuma ba, yana mai cewa al’ummar Gombe sun waye kuma ba za su bari a yi wasa da ƙuri’unsu ba.

Tsohon ministan ya ƙara da kira ga masu kaɗa ƙuri’a da su fito su zaɓi wanda suka ga ya dace ba tare da tsoro ko razana ba, yana mai bayyana cewa PDP na da ƙwarin gwiwar samun nasara ta hanyar zaɓe na gaskiya.

A ƙarshe, Pantami ya soki gwamnatin APC a jihar kan abin da ya kira gazawa wajen inganta rayuwar al’umma, tare da zargin cewa ana bai wa tsirarun mutane kwangilolin gwamnati, sannan ya gode wa magoya bayansa bisa ci gaba da mara masa baya gabanin zaɓen 2027.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *