Mutane 49 sun mutu a hamadar Agadez bayan da motarsu ta ɓace hanya

0
Mutane 49 sun mutu a hamadar Agadez bayan da motarsu ta ɓace hanya

Mutane 49 sun mutu a hamadar Agadez bayan da motarsu ta ɓace hanya

Spread the love

Aƙalla mutane 49 ne suka mutu a hamadar Asamaka da ke Jihar Agadez na Jamhuriyar Nijar, bayan motar da suke ciki ta ɓace hanya sannan ta lalace a tsakiyar hamada.

Rahotanni sun nuna cewa waɗanda abin ya shafa sun shafe lokaci mai tsawo ba tare da samun ruwa ko taimako ba, lamarin da ya sa ake zargin sun rasu sakamakon ƙishirwa da tsananin zafin rana.

Sai dai mutane biyu sun yi nasarar tsira daga wannan ibtila’in, yayin da hukumomi ke ci gaba da bincike kan yadda lamarin ya faru da kuma matakan da za a ɗauka domin kauce wa irin wannan mummunan al’amari a nan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *