Man City ta lallasa Liverpool da ci 3-0, ta tsere wa Arsenal da maki uku a teburin EPL
Man City ta lallasa Liverpool da ci 3-0, ta tsere wa Arsenal da maki uku a teburin EPL
Ƙungiyar Manchester City ta lallasa Liverpool da ci 3-0 a filin Anfield ranar Lahadi, inda ta ƙara ƙarfafa matsayinta na farko a teburin gasar Premier ta Ingila (EPL), bayan samun nasara a wasanninta shida na farko a kakar bana.
Nasarar ta sa City ta hada maki 18, tana gaban Arsenal da maki uku.
A farkon wasan, ƙungiyoyin biyu sun fafata sosai, amma al’amura sun sauya bayan an kori ɗan wasan Liverpool, Ryan Gravenberch, sakamakon katin gargadi na biyu da ya samu.
Erling Haaland ne ya fara zura ƙwallo a ragar Liverpool a minti na 65, kafin Jeremy Doku ya ƙara ta biyu bayan mintuna uku da bugun da ya aika cikin raga mai kayatarwa.
Rayan Cherki ne ya kammala cin ukun a minti na 78, inda City ta tabbatar da nasarar da ta samu a gidan abokiyar hamayyarta.
Nasarar ta ci gaba da riƙe Manchester City a saman teburin EPL da maki 18, yayin da Arsenal ke biye da ita da maki 15.
A gefe guda, Liverpool ta sha kaye a karon farko a gasar bana, lamarin da ya sa ta koma matsayi na tara a teburin gasar.
