Atiku ya yi gargadi kan naɗin jami’an Yoruba a manyan muƙaman INEC gabanin zaɓen 2027
Atiku ya zargi Tinubu da yin watsi da ’yan sandan da suka yi ritaya
Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya nuna damuwa kan naɗin wasu jami’ai biyu ’yan asalin Yarabawa a muhimman sassan Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Atiku, ta bakin mai magana da yawunsa, Phrank Shaibu, ya tambayi dalilan naɗin Oluyemi Titilayo Adeyemi-Showunmi a matsayin shugabar sashen gudanar da zaɓe, da kuma Dr Lawrence Bayode a matsayin shugaban sashen fasahar sadarwa (ICT) na hukumar.
Ya buƙaci INEC ta bayyana ƙa’idojin da ta bi wajen naɗin jami’an domin tabbatar da gaskiya da adalci.
Haka kuma, Atiku ya buƙaci INEC ta bayyana sunayen kamfanonin da aka bai wa kwangilar samar da kayayyakin zaɓe masu muhimmanci, hanyoyin bayar da kwangilolin da kuma matakan tsaron da aka tanada.
Ya kuma nemi hukumar ta tabbatar ko ta musanta rahotannin da ke cewa kamfanin Hitech ko wani kamfani mai alaƙa da shi ya samu irin wannan kwangila.
Atiku ya yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya guji tsoma baki cikin harkokin INEC, yana mai cewa dole ne hukumar ta tabbatar da ’yancin kanta da gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci.
Ya kuma yi gargaɗin cewa duk wani yunƙurin maguɗin zaɓe a 2027 zai fuskanci turjiya ta hanyoyin dimokuraɗiyya da doka ta amince da su.
