Majalisar dokokin Adamawa ta samar da sabuwar doka domin kare haƙƙin masu gidaje da masu haya
Kakakin Majalisan dokokin Adamawa Balthiya Wesley
Majalisar Dokokin Jihar Adamawa ta amince da kudirin doka da zai tsara dangantaka tsakanin masu gidaje da masu haya, domin tabbatar da adalci da kare haƙƙoƙin bangarorin biyu.
Kudirin ya kuma tanadi hanyoyin warware rikice-rikicen haya da kuma fayyace nauyin da ke kan masu gida da masu haya.
A cewar ‘yan majalisar, sabuwar dokar za ta kawo ƙarshen yawan takaddama da ake samu kan haya, tare da samar da ingantaccen tsarin da zai tabbatar da cewa kowane ɓangare ya san haƙƙinsa da abin da doka ta tanada a kansa.
Kudirin ya kuma ƙunshi tanade-tanade kan yadda za a gudanar da yarjejeniyar haya, hanyoyin korar mai haya bisa doka, da kuma yadda za a magance sabanin da ka iya tasowa tsakanin masu ruwa da tsaki cikin lumana.
Ana sa ran sabuwar dokar za ta inganta harkokin gidaje a jihar Adamawa, ta samar da kwanciyar hankali ga masu gidaje da masu haya, tare da rage rikice-rikicen da ke da alaƙa da haya idan ta fara aiki a hukumance.
