Mailantarki zai garzaya kotu bayan kin amincewa da sakamakon zaɓen fitar da gwani na PDP a Gombe
Khamisu Mailantarki
Ɗan takarar gwamnan Gombe a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, Khamisu Ahmed Mailantarki, ya bayyana cewa shi ne ya lashe sabon zaɓen fitar da gwani da jam’iyyar ta gudanar a jihar, duk da cewa an ayyana Farfesa Isa Ali Pantami a matsayin wanda ya samu tikitin jam’iyyar.
Da yake jawabi ga manema labarai jim kaɗan bayan an sanar da sakamakon zaɓen, Mailantarki ya bayyana cewa bisa ga hukuncin kotun ƙoli, Pantami bai kamata ya shiga zaɓen ba. ya kuma ce zai sake komawa kotu domin kalubalantar sakamakon.
Rahotanni sun ce Pantami ya samu ƙuri’u 2,054, yayin da Mailantarki ya samu 389, shi kuma Usman Aliyu Garry ya samu 112. An gudanar da zaɓen kai tsaye a rumfunan jam’iyya da ke faɗin ƙananan hukumomi 11 na jihar Gombe, kafin kwamitin zaɓen ya tattara tare da bayyana sakamakon a hedikwatar PDP ta jihar.
Sabon zaɓen ya biyo bayan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe na ranar 24 ga Satumba, 2026, wanda ya soke zaɓen farko da ya bai wa Pantami tikitin PDP, tare da umartar jam’iyyar da ta sake gudanar da zaɓen cikin kwanaki 30. Kotun ta ce an samu matsaloli wajen bin ƙa’idojin jam’iyyar da tanade-tanaden dokokin zaɓe a tsarin farko.
Sai dai bayan kammala sabon zaɓen, Mailantarki ya nuna cewa har yanzu yana ƙalubalantar tsarin, inda ya yi barazanar sake ɗaukar matakin shari’a kan batun. Wannan na nuni da cewa rikicin tikitin PDP a Gombe na iya ci gaba da kasancewa a gaban kotuna, yayin da Pantami ya sake samun tikitin jam’iyyar a sabon zaɓen.
