Kakakin majalisar Kebbi, Muhammad Ankwai ya rasu
Kakakin majalisar Kebbi, Muhammad Ankwai
Kakakin majalisar dokokin jihar Kebbi, Muhammad Usman Ankwai, ya rasu, lamarin da ya jefa al’ummar jihar da ‘yan siyasa cikin jimami.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Ankwai ya rasu ne a daren ranar Litinin, bayan fama da rashin lafiya, yayin da yake karɓar magani a ƙasar Masar.
Marigayin, wanda ke wakiltar mazabar Zuru a ƙarƙashin jam’iyyar APC, ya kasance ɗaya daga cikin manyan ‘yan siyasa masu tasiri a jihar Kebbi.
Rasuwarsa ta jawo alhini daga shugabanni, ‘yan majalisa da al’ummar jihar, yayin da ake ci gaba da jiran sanarwar hukuma kan shirye-shiryen jana’izarsa da kuma matakin da za a ɗauka game da shugabancin majalisar.
