Gwamna Radda ya gana da al’umma daga mazabu 361 domin tattauna tsarin kasafin kuɗin 2027

0
Gwamna Radda ya gana da al'umma daga mazabu 361 domin tattauna tsarin kasafin kuɗin 2027

Gwamna Radda ya gana da al'umma daga mazabu 361 domin tattauna tsarin kasafin kuɗin 2027

Spread the love

Gwamnatin Jihar Katsina ta fara tarukan tuntubar al’umma a dukkan mazabu 361 domin tattara ra’ayoyin jama’a wajen shirya kasafin kuɗin shekarar 2027.

Gwamna Dikko Umaru Radda ya ce shirin zai bai wa kowane ɗan ƙasa damar bayyana muhimman buƙatun yankinsa domin gwamnati ta ba su fifiko a kasafin kuɗi.

Ya bayyana cewa irin wannan tsarin ya taimaka wajen tsara kasafin kuɗin 2026, wanda ya haifar da aiwatar da ayyuka a fannoni kamar ilimi, lafiya, noma, ruwa da ababen more rayuwa.

Gwamnan ya kuma buƙaci mata, matasa da sauran al’umma su shiga cikin tarukan domin tabbatar da cewa kasafin kuɗin 2027 ya dace da ainihin buƙatun jama’ar jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *