Binciken mu ya nuna mana Tinubu zai lashe zaɓen shugaban kasa na 2027 – Shugaban APC

0
Binciken mu ya nuna mana Tinubu zai lashe zaɓen shugaban kasa na 2027 - Shugaban APC

Binciken mu ya nuna mana Tinubu zai lashe zaɓen shugaban kasa na 2027 - Shugaban APC

Spread the love

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya bayyana kwarin gwiwar cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027, yana mai cewa binciken ra’ayin jama’a da jam’iyyar ta gudanar a jihohi daban-daban ya nuna tana kan gaba.

Yilwatda ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels TV, inda ya ce sakamakon binciken da suka gudanar ya ba su kwarin gwiwar cewa Tinubu zai yi nasara a zaɓen mai zuwa.

Ya kuma ce APC ba ta tsoron jam’iyyun adawa, musamman ADC mai ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da NDC mai ɗan takarar ta, Peter Obi.

Shugaban APC ɗin ya kuma kare manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu, yana mai cewa sauye-sauyen haraji da aka aiwatar za su ƙara kuɗaɗen shiga na gwamnati tare da taimaka wa masu ƙaramin ƙarfi.

Ya kuma yi iƙirarin cewa sauye-sauyen da aka samu a ɓangaren wutar lantarki sun bai wa gwamnatocin jihohi damar samarwa da rarraba wutar lantarki.

Sai dai Yilwatda ya amince cewa ’yan Najeriya na fuskantar matsin tattalin arziki sakamakon tsadar man fetur, amma ya bayyana halin da ake ciki a matsayin na ɗan lokaci.

Ya kuma yi watsi da zargin cewa APC na kare mambobinta daga fuskantar shari’a kan zarge-zargen rashawa, yana mai cewa wasu ’ya’yan jam’iyyar na fuskantar shari’a a kotuna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *