Ba zan halarci yaƙin neman zaɓe a dukkan jihohi ba kada ya ɗauke min hankali daga gudanar da mulkin ƙasa – Tinubu

0
Ba zan halarci yaƙin neman zaɓe a dukkan jihohi ba kada ya ɗauke min hankali daga gudanar da mulkin ƙasa - Tinubu

Ba zan halarci yaƙin neman zaɓe a dukkan jihohi ba kada ya ɗauke min hankali daga gudanar da mulkin ƙasa - Tinubu

Spread the love

Shugaban Ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya nuna cewa mai yiwuwa ba zai halarci dukkan tarukan yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC a faɗin jihohin ƙasar ba gabanin zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Tinubu ya ce ya amince da shawarar shugabannin jam’iyyar na kada ayyukan yaƙin neman zaɓe su ɗauke masa hankali daga gudanar da mulkin ƙasa, yana mai jaddada cewa Najeriya na buƙatar kulawa sosai a halin da ake ciki.

Ya kuma bayyana cewa nauyin gudanar da gwamnati da kuma biyan basussukan ƙasa na daga cikin dalilan da za su hana shi zagayawa dukkan jihohin ƙasar domin kamfen.

Sai dai shugaban ƙasar ya tabbatar da cewa har yanzu zai riƙa samun lokacin tattaunawa kai tsaye da ’yan Najeriya, yayin da shugabannin APC da mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen za su jagoranci wayar da kan masu zaɓe a jihohi da ƙananan hukumomi.

Ya buƙaci kwamitin da ya isar da manufofin jam’iyyar, nasarorin gwamnatinsa da shirye-shiryenta ga al’umma a faɗin ƙasar.

Tinubu ya kuma bayyana kwamitin yaƙin neman zaɓen a matsayin wata hanya ta sabunta alƙawarin APC ga al’ummar Najeriya, yana mai cewa jam’iyyar a shirye take domin tunkarar zaɓen 2027.

Wannan mataki na zuwa ne yayin da jam’iyyar ke ƙara shirye-shiryen yaƙin neman zaɓen sake zaɓen Tinubu, inda ake sa ran kwamitin zai taka muhimmiyar rawa wajen tsara kamfen da tattara goyon bayan masu zaɓe a faɗin ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *