Dele Momodu ya zargi Tinubu da cika INEC da ’yan kabilar Yarbawa
Dele Momodu ya zargi Tinubu da cika INEC da ’yan kabilar Yarbawa
Dele Momodu, jigo a jam’iyyar ADC, ya zargi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da naɗa mutane da dama daga yankin Kudu maso Yammacin Najeriya, musamman ’yan kabilar Yarbawa, a muhimman muƙamai a Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), lamarin da ya ce na iya haifar da shakku kan adalcin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Momodu ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Arise News, inda ya nuna damuwa kan yiwuwar gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.
Ya ce mutane da dama, har da wasu magoya bayan shugaban ƙasar, na shakkun ko za a gudanar da zaɓen cikin ’yanci da adalci.
Ya kuma yi zargin cewa tsoron da wasu gwamnoni, alkalai da ’yan majalisa ke yi wa shugaban ƙasar na iya raunana tsarin da ya kamata ya tabbatar da daidaito da kuma sa ido kan ayyukan gwamnati.
Sai dai waɗannan kalamai zarge-zarge ne da Momodu ya yi, ba hujjar da ta tabbatar da an yi maguɗi a zaɓe ba.
Sai dai jigon na ADC ya ce jam’iyyarsa na aiki a bayan fage domin hana Tinubu samun wa’adi na biyu a zaɓen 2027, amma ya ƙi bayyana dabarun da suke shirin amfani da su.
Ya jaddada cewa ’yan Najeriya na da rawar da za su taka wajen tabbatar da sakamakon zaɓe da kuma sauyin gwamnati ta hanyar dimokuraɗiyya.
