Atiku yana sukar Gwamnatin Tinubu ne saboda zafin rashin nasara a zaɓen 2023 – Keyamo
Atiku yana sukar Gwamnatin Tinubu ne saboda zafin rashin nasara a zaɓen 2023 - Keyamo
Ministan Sufurin Jiragen sama na Najeriya, Festus Keyamo, ya zargi tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, da munafunci, bisa sukar da yake yi wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu gabanin zaɓen shekarar 2027.
Keyamo ya bayyana cewa sukar da Atiku ke yi wa shugaban ƙasar na baya-bayan nan ta samo asali ne daga rashin jin daɗin nasarar da Tinubu ya samu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Rikicin na zuwa ne bayan Atiku ya soki matakin gwamnatin tarayya na rage farashin man fetur na tsawon kwanaki 30 a gidajen mai na Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC), inda ya bayyana matakin a matsayin wata dabara ta neman tallata gwamnati, maimakon samar da mafita mai ɗorewa ga matsin tattalin arzikin da ’yan Najeriya ke fuskanta.
Keyamo ya yi zargin cewa Atiku na nuna ɓacin rai ne saboda Tinubu ya samu nasarar zama shugaban ƙasa, duk da cewa shi Atiku ya daɗe yana neman wannan kujera.
Ya kuma yi iƙirarin cewa sukar da tsohon mataimakin shugaban ƙasar ke yi wa gwamnati ba ta rasa nasaba da rashin gamsuwa da sakamakon siyasar da ta kai Tinubu ga shugabancin ƙasa.
Ministan ya kuma yi kira ga mutanen da ke kusa da Atiku da su taimaka masa maimakon ƙarfafa shi wajen ci gaba da sukar shugaban ƙasa.
Ya bayyana cewa Atiku na buƙatar goyon baya a wannan lokaci, yana mai cewa yana ganin tsohon mataimakin shugaban ƙasar na fuskantar koma baya a siyasance yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.
