Atiku ya kaddamar da shafin Intanet da ’yan Najeriya za su riƙa yi masa tambayoyi gabanin zaɓen 2027
Atiku ya zargi Tinubu da yin watsi da ’yan sandan da suka yi ritaya
Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya ƙaddamar da wani shafin intanet mai suna “Ask AA”, domin bai wa ’yan Najeriya damar yi masa tambayoyi kai tsaye kan tarihinsa a siyasa, manufofinsa da shirye-shiryensa na tafiyar da ƙasar, yayin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.
Shafin, wanda aka tsara zai fara aiki da ƙarfe 8:30 na daren Alhamis, 15 ga Oktoba, 2026, zai bai wa jama’a damar gabatar da tambayoyi kan tattalin arziki, tsaro, fasaha, samar da ayyukan yi da hanyoyin rage tsadar rayuwa a Najeriya.
Daraktan yaɗa labarai da sadarwa na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar ADC, Phrank Shaibu, ne ya bayyana ƙaddamar da shafin a cikin wata sanarwa.
Atiku ya ce yana son ’yan Najeriya su riƙa yi masa tambayoyi, su bayyana ra’ayoyinsu kan manufofinsa tare da gabatar da shawarwarin da za su taimaka wajen ci gaban ƙasa.
Atiku ya kuma bayyana cewa zai kira wasu daga cikin mutanen da suka gabatar da tambayoyi ta wayar tarho, musamman waɗanda suka bayar da lambobin wayoyinsu, domin jin ƙorafinsu da matsalolin da suke fuskanta.
Ƙaddamar da shafin na zuwa ne yayin da Atiku, wanda ke neman shugabancin ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, ke shirin tunkarar zaɓen 2027.
