Allah ya yi wa Tsohon Manajan Adam A. Zango, Bature Zambuk, rasuwa

0
Spread the love

An sanar da rasuwar Bature Zambuk, tsohon manajan fitaccen jarumin masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, Adam A. Zango, wanda ya rasu a yau a Jihar Bauchi.

Sanarwar rasuwar marigayin ta fito ne ta hannun abokin aikinsa, Usman Muazu, wanda ya wallafa saƙon alhini, inda ya bayyana Bature Zambuk a matsayin ɗan’uwa kuma abokin aiki da ya yi mu’amala da shi a harkokin sana’a.

Bature Zambuk ya shahara wajen gudanar da harkokin manajanci ga mawaka da jarumai, tare da bayar da gudummawa a masana’antar Kannywood, musamman a ɓangaren gudanarwa da shirya fina-finai.

Rasuwarsa ta jefa abokan aikinsa da sauran waɗanda suka san shi cikin alhini, yayin da ake jimamin rashin abokin sana’a da ya bayar da tasa gudummawa wajen bunƙasa masana’antar fina-finan Hausa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *