NEMA da ADSEMA sun raba kayan abinci ga gidaje 1,000 a Adamawa

0
IMG-20260713-WA0002
Spread the love

Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) tare da hadin gwiwar Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Adamawa (ADSEMA) sun raba kayan tallafin abinci ga gidaje 1,000 masu rauni daga al’ummomin Hulere, Sangere Bode da Ngurore, da kuma wasu ‘yan gudun hijirar da suka koma zama cikin al’ummomi a jihar.

Shugaban Ayyuka na NEMA mai kula da jihohin Adamawa da Taraba, Mista Ladan Ayuba, ya ce tallafin wani shiri ne na gwamnatin tarayya domin rage radadin matsin tattalin arziki da ke addabar marasa galihu, musamman masu bukata ta musamman da ‘yan gudun hijira.

Shugaban Kungiyar Masu bukata ta musamman reshen jihar Adamawa, Kwamared Abdullahi Toungo, ya yabawa shirin, yana mai cewa tallafin ya zo a lokacin da ya fi dacewa.

Ya kuma bukaci gwamnati ta fadada irin wannan tallafi zuwa sauran al’ummomin da ba su amfana ba.

Kayan tallafin sun hada da buhunan shinkafa da wake na kilo 25, galan din man gyada mai lita hudu, Maggi da tumatir na gwangwani.

Wadanda suka amfana sun nuna godiya ga NEMA da ADSEMA, yayin da aka gudanar da rabon cikin tsari da lumana karkashin kulawar jami’an tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *