Harin Rasha ya kashe dalibar likitanci ƴar Najeriya kwana guda kafin ta karɓi takardan digiri
Wata ‘yar Najeriya mai suna Nnani Adaobi Marian mai shekaru 23, wadda ke karatun likitanci a matakin ƙarshe a birnin Kharkiv na ƙasar Ukraine, ta rasu sakamakon munanan raunukan da ta samu a harin sama da Rasha ta kai. Lamarin ya faru ne kwana guda kafin ranar da aka shirya ba ta takardar digirinta bayan kammala karatu.
Rahotanni sun ce harin ya auku ne a ranar 29 ga watan Yuni, lokacin da Adaobi tare da wata abokiyarta Fatima Huseynova ke kan hanyarsu ta zuwa ɗaukar hotunan bikin kammala karatu. Fatima ta mutu nan take, yayin da Adaobi ta samu munanan raunuka kafin daga bisani ta rasu a wani asibiti da ke Jamus, duk da ƙoƙarin da likitoci suka yi na ceto rayuwarta.
Jami’ar Kharkiv National Medical University ta bayyana Adaobi a matsayin ɗaliba mai hazaka, tawali’u da son taimakon al’umma. Ta kuma bayyana cewa ta yi horo a jami’o’i da cibiyoyin lafiya na ƙasashen Birtaniya da Turkiyya, inda ta nuna ƙwazo a fannin likitanci.
Mutuwar Adaobi ta sake jawo hankalin duniya kan irin haɗarin da yaƙin Rasha da Ukraine ke ci gaba da haifarwa ga fararen hula da kuma ɗaliban ƙasashen waje da ke zaune a Ukraine, musamman waɗanda ke fatan kammala karatunsu cikin lumana.
