Gwamnatin Yobe ta fara sabon shiri na dakile barkewar cutar Kolera

0
Mai Mala Buni
Spread the love

Gwamnatin Jihar Yobe, ta hannun Hukumar Kula da Lafiya ta Matakin Farko, tare da haɗin gwiwar Lafiya UK da abokan hulɗa, ta ƙara ƙaimi wajen inganta shirye-shiryen kariya da dakile yaɗuwar cutar kolera a faɗin jihar.

A wani taro da aka gudanar a Damaturu, jami’an wayar da kan jama’a kan lafiya da jami’an sa ido kan cututtuka daga ƙananan hukumomi 17 sun tattauna kan hanyoyin sadarwa, haɗa kan al’umma da kuma inganta tsarin sa ido kan cututtuka.

Da yake buɗe taron, Daraktan Sashen Lafiyar Iyali da Al’umma na YSPHCB, Alhaji Ibrahim Maikasuwa, ya tabbatar da kudirin gwamnatin jihar na ƙarfafa tsarin rigakafi da kuma gaggauta ɗaukar matakan dakile barkewar cututtuka.

A nasa jawabin, Alhaji Bulama Yaro ya jaddada muhimmancin wayar da kan jama’a, isar da sahihan bayanai cikin lokaci da kuma ingantaccen sa ido a matsayin manyan hanyoyin da za su taimaka wajen shawo kan cutar kolera.

Ƙungiyar Lafiya UK, tare da wakilan WHO da UNICEF, sun sake tabbatar da ci gaba da tallafa wa Jihar Yobe domin inganta harkokin lafiya da ƙarfafa shirin yaƙi da barkewar cututtuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *