An ceto daliban NECO da malamai 10 bayan harin ISWAP a makarantar Borno
An ceto daliban NECO da malamai 10 bayan harin ISWAP a makarantar Borno
Dakarun Operation HADIN KAI sun samu nasarar ceto ɗaliban jarabawar NECO da malamai guda 10 da wasu da ake zargin mayakan ISWAP ne suka yi garkuwa da su bayan kai hari kan makarantar Technical Secondary School da ke garin Lassa, ƙaramar hukumar Askira/Uba a Jihar Borno.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 9:00 na safiyar ranar Litinin, a lokacin da ɗalibai ke rubuta jarabawar NECO, inda suka sace wasu daga cikin ɗaliban da malamansu kafin su tsere zuwa cikin dazukan da ke kewaye da garin.
Bayan samun rahoton harin, dakarun Operation HADIN KAI sun ƙaddamar da samame cikin gaggawa domin bin sawun maharan, lamarin da ya kai ga ceto mutane 10 daga cikin waɗanda aka sace tare da mayar da su cikin aminci.
Ana ci gaba da gudanar da bincike da kuma farautar sauran maharan domin ceto duk waɗanda har yanzu suke hannunsu, yayin da jami’an tsaro suka tabbatar da ƙudirin su na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a yankin Arewa maso Gabas.
