2027: Tinubu ba zai amince da shan kaye ba, amma za mu kore shi – Dele Momodu
2027: Tinubu ba zai amince da shan kaye ba, amma za mu kore shi – Dele Momodu
Wani jigo a jam’iyyar ADC, Dele Momodu, ya bayyana shakku kan yiwuwar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gudanar da zaɓen 2027 cikin gaskiya da adalci, yana mai cewa hatta wasu daga cikin magoya bayan shugaban ƙasar ba su yarda da hakan ba.
Momodu ya ce akwai fargabar cewa idan Tinubu ya sha kaye a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, ba zai amince ya miƙa mulki ga wanda ya yi nasara ba. Sai dai ya jaddada cewa ’yan Najeriya za su yi tsayin daka domin tabbatar da sauyin gwamnati idan hakan ta faru.
Da yake magana a shirin siyasa na gidan talabijin na Arise News, Momodu ya ce ba wai mambobin ADC kaɗai ne ke son ganin Tinubu ya bar mulki ba, har ma da talakawan da suke ganin ba sa son ya sake samun wa’adi na biyu.
Ya kuma yi zargin cewa wasu gwamnoni, alkalai da ’yan majalisa suna fuskantar matsin lamba, yana mai cewa wasu ’yan siyasa na aiki a bayan fage domin hana Tinubu sake lashe zaɓen 2027.
