Yobe ta fara sabbin matakan dakile mace-macen mata da yara
Yobe ta fara sabbin matakan dakile mace-macen mata da yara
Hukumar Kula da Lafiya ta Matakin Farko ta Jihar Yobe (YSPHCB) ta gudanar da taron bitar zangon biyu na shekarar 2026 kan sa ido da bibiyar mace-macen mata da yara domin inganta ayyukan kiwon lafiya a faɗin jihar.
Taron ya gudana a dakin taro na Dr. Umar Chiroma ƙarƙashin jagorancin Babban Sakataren Hukumar, Dakta Babagana Kundi Machina.
Daraktan Sashen Lafiyar Iyali da Al’umma, Alhaji Ibrahim Maikasuwa fsi, wanda ya wakilci Babban Sakataren Hukumar, ya bayyana cewa shirin MPCDSR na da muhimmanci wajen rage mace-macen mata masu juna biyu, jarirai da yara a jihar.
Ya ce taron na bai wa masu ruwa da tsaki damar nazarin nasarori da matsalolin da ake fuskanta domin ɗaukar matakan gyara.
A yayin taron, jami’an lafiya sun gabatar da rahotannin bayanai na zangon farko na shekarar 2026, inda suka yi bayani kan yadda ake gudanar da sa ido, tattara bayanai da matakan magance mace-macen mata da jarirai a cibiyoyin lafiya da ƙananan hukumomi.
Wakilan ƙananan hukumomi da jami’an Ma’aikatar Lafiya ta jihar sun jaddada muhimmancin bayar da rahoto cikin lokaci, inganta tsarin gaggawa da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki domin kare lafiyar mata da yara a jihar Yobe.
