Jami’ar AUN za ta yaye dalibai cikin ƴan matan Chibok 12 da suka kammala karatu
Jami’ar American University of Nigeria (AUN) da ke Yola za ta yi biki na musamman a ranar 9 ga Mayu, 2026, yayin da ‘yan matan Chibok guda 12 da aka ceto daga hannun ‘yan ta’adda za su kammala karatunsu.
Wannan lamari na nuni da nasarar ilimi da juriyar rayuwa kan ta’addanci, bayan shekaru na wahala da ƙalubale da waɗannan mata suka fuskanta.
Shugaban jami’ar, DeWayne Frazier, ya bayyana cewa wannan bikin yaye dalibai ba wai kawai nasarar karatu ba ce, illa alama ce ta nasarar ilimi kan akidar ƙungiyar Boko Haram wadda ke adawa da ilimi.
Ya ce wannan rana za ta kasance mai cike da muhimmaci, domin tana nuna yadda aka dawo da mutunci da darajar waɗannan mata.
A cewarsa, lokacin da waɗannan ‘yan mata za su hau mataki domin karɓar shaidar kammala karatu, hakan zai zama wata babbar alama ta nasara, inda ya jaddada cewa duniya ta yi kira da a dawo da su, amma yanzu ana tura su gaba a matsayin mata masu ilimi da ƙarfin gwiwa domin gina makoma mai kyau.
