Fintiri ya jinjina wa Malaman Adamawa tare da Alkawarin tabbatar da ci gaba da Inganta bangaren Ilimi

0
Gwamna Fintiri ya ce Adamawa ta zama jiha mai goyon bayan Tinubu 100% inda ya yi hasashen nasarar APC a 2027

Gwamna Fintiri

Spread the love

Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya taya malamai a fadin jihar murnar zagayowar Ranar Malamai ta Duniya ta 2026, tare da bayyana irin muhimmiyar gudummawar da suke bayarwa wajen gina al’umma da shirya matasa domin makomar gaba.

Gwamnan ya ce malamai ba wai koyar da darasi kawai suke yi ba, har ma suna taimakawa wajen gano baiwar yara, gina halayensu da kuma dasa musu ilimi da kishin ci gaba.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ma’aikatar Yada Labarai da Dabaru ta jihar, Leader Leneke, JP, ya fitar, gwamnatin ta bayyana cewa malamai sun taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban Adamawa, tun daga zamanin baya har zuwa yanzu.

Sanarwar ta kuma yi tsokaci kan Malam Gilamdo Yohanna Kwem na Government Girls Secondary School, Yola, wanda ya samu karramawa a matakin kasa saboda kwazonsa a aikin koyarwa, tana mai cewa nasararsa shaida ce kan irin hazaka da kwarewar malamai a jihar.

Gwamna Fintiri ya ce ci gaban da ake samu a bangaren ilimi, ciki har da ingantaccen sakamakon dalibai a matakin firamare da sakamakon jarabawar WAEC da NECO, baya rasa nasaba da kokarin malamai da ma’aikatan ilimi.

Ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da ba ilimi fifiko, tare da daukar matakai wajen inganta wuraren koyarwa, karfafa cibiyoyin ilimi da inganta jin dadin malamai, horas da su da kuma bunkasa kwarewarsu.

Gwamnan ya bukaci malaman Adamawa da su ci gaba da jajircewa wajen gudanar da aikinsu na koyar da yara, yana mai cewa tasirin aikin malami na iya dorewa har tsawon tsararraki.

Ya ce gwamnatin jihar tana ganin malamai, tana darajarsu kuma tana yaba musu bisa sadaukarwa da jajircewarsu wajen gina al’umma, tare da yi musu fatan samun karin karfi da nasara a wannan muhimmin aiki na koyar da al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *