Remi Tinubu ta kaddamar da gangami na tattara mata waje daya domin goyon bayan Tinubu a zaben 2027
Remi Tinubu ta kaddamar da gangami na tattara mata waje daya domin goyon bayan Tinubu a zaben 2027
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta shiga cikin shugabannin jam’iyyar APC da masu ruwa da tsaki a wajen kaddamar da shirin tattara da karfafa mata na jam’iyyar APC, wanda aka gudanar a ranar Litinin, 5 ga Oktoba, 2026, a Bola Ahmed Tinubu International Conference Center da ke Abuja.
Taron ya hada manyan masu ruwa da tsaki mata na APC, ‘yan takarar mata da kuma mambobin sashen tattara mata na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC na 2027.
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai matar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Hajiya Nana Shettima; Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC, Sanata Abdulaziz Yari; Gwamnan Imo, Sanata Hope Uzodimma, da tsohon Shugaban APC na ƙasa, Umar Abdullahi Ganduje.
Wani muhimmin bangare na taron shi ne rabawa mata masu cin gajiyar shirin kayayyakin tallafi daban-daban domin taimaka musu wajen bunkasa sana’o’insu da inganta rayuwarsu.
Sanata Oluremi Tinubu da kanta ta gabatar da wasu daga cikin kayayyakin, ciki har da babur da aka bai wa daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin.
Bayan kammala taron, Uwargidan Shugaban Ƙasar ta gudanar da ganawar sirri da wasu ‘yan takarar mata na APC da sauran manyan baki.
Shirin na daga cikin kokarin jam’iyyar na kara hada kan mata da kuma karfafa shigarsu cikin harkokin siyasa, yayin da ake tunkarar babban zaben Najeriya na 2027.
