INEC za ta fitar da sabbin bayanai kan shirye-shiryen zaben 2027 da ya rage kwanaki 100

0
INEC za ta dauki mataki kan ’yan takara masu saba dokar zaɓe bayan hukuncin kotun koli

INEC za ta fitar da sabbin bayanai kan shirye-shiryen zaben 2027 da ya rage kwanaki 100

Spread the love

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce za ta bayyana cikakken bayani kan shirye-shiryenta na babban zaben 2027, yayin da aka fara kirga kwanaki 100 kafin zaben.

Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, SAN, zai jagoranci taron manema labarai da masu ruwa da tsaki, inda ake sa ran hukumar za ta yi bayani kan rajistar masu kada kuri’a, tantance ‘yan takara da shirye-shiryen kayan aikin zabe.

Taron zai hada da shugabannin jam’iyyun siyasa, jami’an tsaro, kungiyoyin farar hula, masu sa ido kan zabe, wakilan kasashen waje da sauran masu ruwa da tsaki.

A jadawalin da INEC ta fitar, za a gudanar da zaben Shugaban Kasa da na ‘yan Majalisar Dokoki ta Tarayya a ranar 16 ga Janairu, 2027, yayin da zaben gwamnoni da na majalisun jihohi zai kasance ranar 6 ga Fabrairu, 2027.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *