IHRC ta yi Allah-Wadai da zargin cin zarafin yar makaranta mai shekaru 7 a Adamawa

0
 IHRC ta yi Allah-Wadai da zargin cin zarafin yar makaranta mai shekaru 7 a Adamawa

 IHRC ta yi Allah-Wadai da zargin cin zarafin yar makaranta mai shekaru 7 a Adamawa

Spread the love

Kungiyar International Human Rights Commission (IHRC), ofishin Najeriya na Yola, ta bayyana damuwa tare da yin Allah-wadai da zargin cin zarafin wata yarinya mai shekaru bakwai, dalibar aji na biyu a makarantar firamare ta Damilu 2 da ke Jihar Adamawa.

A cikin wata sanarwa da IHRC ta fitar, ta ce ana zargin wani malamin ajin yarinyar da aikata laifin, lamarin da mahaifiyar yarinyar ta kai rahoto ga hukumomi a ranar 30 ga Satumba, 2026.

Kungiyar ta ce Sashen Leken Asiri na Jiha (SID) da Rundunar ’Yan Sandan Jihar Adamawa sun fara daukar matakan da suka dace domin gudanar da bincike.

IHRC ta yaba wa Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Adamawa bisa kulawa da lamarin da kuma daukar matakan da suka dace, tana kuma kira da a ba yarinyar kariya, a gudanar da bincike cikin kwarewa, sannan a tabbatar an samar mata da kulawar lafiya da ta fuskar tunani.

Ta kuma bukaci hukumomin da abin ya shafa su hada kai domin tabbatar da bin ka’ida da kare hakkin yarinyar.

Kungiyar ta kuma yi kira ga kafafen yada labarai da jama’a da su kare sirrin yarinyar, tare da gargadin kada a yada sunanta, hotonta, adireshinta, bayanan makaranta ko wani abu da zai iya bayyana asalinta. IHRC ta ce za ta ci gaba da bibiyar lamarin a karkashin aikinta na kare hakkin dan Adam da yara, tare da tabbatar da cewa tsaro, mutunci da maslahar yarinyar su kasance kan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *