Jami’ar Modibbo Adama ta yi bikin marabtan sabbin dalibai 8,591

0
Jami’ar Modibbo Adama ta yi bikin marabtan sabbin dalibai 8,591

Daliban jami'ar Modibbo Adama

Spread the love

Jami’ar Modibbo Adama University da ke Yola a Jihar Adamawa ta yi bikin ɗaukar sabbin ɗalibai 8,591 na zangon karatu na 2025/2026.

Shugaban jami’ar, Ibrahim Umar, ya taya ɗaliban murna tare da ƙarfafa su da su mai da hankali kan karatu, ladabi da kuma neman ilimi mai amfani.

Ya kuma yi gargaɗi cewa jami’ar ba za ta lamunci satar amsa a jarrabawa, shan miyagun ƙwayoyi da sauran munanan ɗabi’u ba, yana mai cewa duk wanda aka kama zai fuskanci hukunci mai tsauri.

Haka kuma, ya bayyana cewa jami’ar ta karɓi ɗalibai 132 daga ƙasashen waje, tare da ƙara sabbin fannoni da kwalejoji domin inganta harkokin karatu.

A ɓangaren ci gaba, jami’ar ta samar da wutar lantarki ta hasken rana na awanni 24, tare da shirin ƙara ɗakunan kwanan ɗalibai duk da ƙalubalen masauki da ake fuskanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *