Fintiri ya yi afuwa ga fursunoni tara tare da sauya wa wasu hukuncin kisa zuwa daurin rai da rai
Fintiri ya yi afuwa ga fursunoni tara tare da sauya wa wasu hukuncin kisa zuwa daurin rai da rai
Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya yi afuwa tare da bayar da umarnin sakin fursunoni tara da ke zaman gidan gyaran hali daban-daban a jihar, a yayin bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin Najeriya.
Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan, Humwashi Wonosikou, ya ce an dauki matakin ne bisa shawarar Kwamitin Ba da Shawarar Afuwa, da kuma ikon da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya bai wa gwamna a karkashin Sashe na 212(1)(d).
Fursunonin da aka yi wa afuwar sun hada da Abubakar Dajo da ke gidan gyaran hali na Maximum Security Custodial Centre da ke Jos, da Zabadi Ayuba da Salvation Nyamso da ke Numan.
Sauran su ne Amir Idris, Mohammed Saidu, Yaro Sambo, Buhari Salisu, Urube Samuel da Bamaiyi Amos, wadanda ke cibiyoyin gyaran hali na Jimeta, Ganye, Guyuk, Yola Old da Kojoli.
Wonosikou ya bayyana cewa Gwamna Fintiri ya dauki matakin ne domin nuna murna da ranar ’yancin kai ta Najeriya ta shekarar 2026. Ya ce afuwar da sauya hukuncin za su fara aiki nan take, bayan kammala dukkan matakan doka tare da Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya.
A gefe guda, Gwamna Fintiri ya amince da sauya hukuncin kisa da aka yanke wa wani fursuna, Saidu Abdullahi na gidan gyaran hali na Yola Old, zuwa daurin rai da rai.
