Ma’aikatan Gwamnati a Najeriya sun fara yajin aikin gargadi na kwanaki uku

0
Ma’aikatan Gwamnati a Najeriya sun fara yajin aikin gargadi na kwanaki uku

Ma’aikatan Gwamnati a Najeriya sun fara yajin aikin gargadi na kwanaki uku

Spread the love

Ma’aikatan hidimar gwamnati karkashin Joint National Public Service Negotiating Council (JNPSNC) sun fara yajin aikin gargadi na kwanaki uku, wanda ya fara daga ranar Juma’a, 2 ga Oktoba, zuwa Lahadi, 4 ga Oktoba, 2026.

Kungiyar ta ce matakin ya biyo bayan abin da ta bayyana a matsayin tsananin matsin tattalin arziki da ke addabar ma’aikata da masu dogaro da su.

A wata sanarwa da sakataren kungiyar, Olowoyo Gbenga, ya sanya wa hannu, an umarci ma’aikatan gwamnati a matakin tarayya, jihohi da kananan hukumomi da su shiga yajin aikin.

Kungiyar ta ce ta dauki matakin ne bayan ta ce gwamnatin tarayya ba ta magance bukatun da ta gabatar a wasikar da ta aika wa Shugaba Bola Tinubu a ranar 21 ga Satumba ba.

Daga cikin manyan bukatun ma’aikatan akwai rage farashin man fetur zuwa Naira 500 kan kowace lita, amincewa da tallafin albashi na musamman ga ma’aikata, da kuma fara shirin tattaunawa kan sabon mafi karancin albashi da ake sa ran zai fara aiki daga shekarar 2027.

Kungiyar ta ce hauhawar farashin kayayyaki, sufuri da sauran bukatun yau da kullum na kara rage karfin siyan ma’aikata.

A cewar kungiyar, yajin aikin na kwanaki uku na nufin jawo hankalin gwamnati kan halin da ma’aikata da sauran ‘yan Najeriya ke ciki, tare da matsa mata lamba ta dauki matakan rage radadin tsadar rayuwa.

A halin yanzu, kungiyar ta tabbatar da cewa yajin aikin zai gudana kamar yadda aka tsara daga 2 zuwa 4 ga Oktoba, 2026.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *