2027: Zan yi wa’adi daya a NNPP, na biyu a APC — Gwamnan Kano

0
2027: Zan yi wa’adi daya a NNPP, na biyu a APC — Gwamnan Kano

Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf

Spread the love

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa zai yi wa’adin mulki na farko ne a jam’iyyar NNPP, sannan ya nemi wa’adi na biyu a jam’iyyar APC.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan taken siyasa na “wa’adi daya” da wasu ke yi masa, inda ya ce hakan ya shafi zamansa a NNPP ne kawai.

Gwamnan ya jaddada cewa sauya sheƙarsa zuwa APC na da alaƙa da muradun al’ummar Kano, tare da nuna cewa jam’iyyar APC ita ce ke da ƙarfin lashe zaɓe a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

Haka kuma, ya nuna kwarin gwiwa kan cewa zai samu goyon bayan jama’a domin komawa wa’adi na biyu a ƙarƙashin APC a zaɓen 2027.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *