2027: Zamu tabbatar cewa an gudanar da zaɓe da zai sa ’yan Najeriya suyi alfahari da ’yan sanda – IG

0
2027: Zamu tabbatar cewa an gudanar da zaɓe da zai sa ’yan Najeriya suyi alfahari da ’yan sanda - IG

2027: Zamu tabbatar cewa an gudanar da zaɓe da zai sa ’yan Najeriya suyi alfahari da ’yan sanda - IG

Spread the love

Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Olatunji Disu, ya bayyana cewa yadda jami’an ’yan sanda za su gudanar da ayyukansu kafin, lokacin da kuma bayan babban zaɓen shekarar 2027 zai sa ’yan Najeriya su yi alfahari da rundunar.

Ya tabbatar da cewa rundunar za ta gudanar da ayyukanta cikin ƙwarewa da kwarewa ta aiki domin tabbatar da ingantaccen zaɓe.

Disu ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan ƙaddamar da littafin The Origin of Women in Nigeria Police Force, wanda wata tsohuwar mataimakiyar kwamishinan ’yan sanda mai shekaru 96, Stella Okuyiga, ta rubuta.

Ya ce rundunar ta gudanar da taron manyan jami’anta, ciki har da kwamishinonin ’yan sanda daga sassa daban-daban na ƙasar, domin nazarin nasarorin da aka samu a zaɓukan baya da kuma gyara kura-kuran da aka tafka.

Ya ce rundunar za ta yi amfani da darussan da ta koya daga zaɓukan da suka gabata wajen inganta ayyukanta a babban zaɓen 2027, wanda ya ce ’yan Najeriya da dama ke sa ran ganin an gudanar da shi cikin nasara.

Ya kuma ba da tabbacin cewa ’yan sanda za su yi ƙoƙarin ganin sun gudanar da aikinsu yadda ya kamata, tare da tabbatar da cewa al’umma sun gamsu da ayyukansu.

Da yake magana kan marubuciyar littafin, Disu ya ce Okuyiga na cikin mata na farko da suka shiga rundunar ’yan sandan Najeriya a shekarar 1955.

Ya bayyana cewa rundunar za ta samar da kwafin littafin ga makarantun horas da ’yan sanda domin jami’ai su koyi tarihin hidimar mata a rundunar tare da amfani da ƙwarewar da suka gada wajen inganta ayyukan tsaro a nan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *