Matawalle ya zargi ƴan adawa da neman goyon bayan kasashen waje don kifar da Tinubu
Matawalle ya zargi ƴan adawa da neman goyon bayan kasashen waje don kifar da Tinubu
Karamin Ministan tsaro na Najeriya, Bello Matawalle, ya zargi wasu jagororin adawa da neman goyon bayan ƙasashen waje domin bata sunan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma ƙoƙarin raunana martabar Najeriya a idon duniya.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun hadimin sa Ahmad Dan Wudil, Matawalle ya ce irin wannan mataki ba ya taimakawa dimokuraɗiyya ko warware matsalolin ƙasa, yana mai kira ga ‘yan adawa su rungumi siyasa mai ma’ana tare da gabatar da mafita ga matsalolin Najeriya.
Ya kuma jaddada cewa shugabancin ƙasa alama ce ta ikon Najeriya da ya kamata a mutunta ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba, yana mai cewa babu wata ƙasa ko kamfanin neman goyon baya da zai iya sauya zaɓin da ‘yan Najeriya suka yi.
Sanarwar Matawalle ta fito ne yayin da siyasar gabanin zaɓen 2027 ke ƙara zafi, inda ya buƙaci dukkan ‘yan siyasa su guji ɗaukar matakan da za su iya tayar da zaune tsaye ko bata sunan Najeriya a ƙasashen waje.
