’Yan takarar Gwamna a Adamawa sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya
’Yan takarar Gwamna a Adamawa sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya
’Yan takarar kujerar gwamnan Jihar Adamawa a zaɓen 2027 sun sanya hannu kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya, inda suka yi alkawarin gudanar da kamfen cikin lumana, tare da mayar da hankali kan manufofi da shirye-shiryen da za su amfani jihar.
An rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a ranar Talata a Banquet Hall na Gidan Gwamnatin Jihar Adamawa da ke Yola.
Yarjejeniyar ta gudana ne a ƙarƙashin taken “Zaman Lafiya Kafin, Lokacin da Bayan Zaɓe”, wanda Gidauniyar ABAK Peace Foundation ta shirya tare da haɗin gwiwar National Peace Committee da Adamawa State Peace Commission.
’Yan takarar sun yi alkawarin guje wa tashin hankali, kalaman ƙiyayya, tunzura jama’a ta fuskar ƙabila ko addini, barazana, yaɗa bayanan ƙarya da kuma kai hare-haren siyasa na kashin kai.
Daga cikin ’yan takarar da suka sanya hannu akwai ɗan takarar jam’iyyar APC, Ahmed Tijjani Galadima.
Masu shirya taron sun ce zaman lafiyar zaɓen 2027 na buƙatar haɗin gwiwar jam’iyyun siyasa, ’yan takara, magoya baya, shugabannin gargajiya da na addini, jami’an tsaro, ƙungiyoyin fararen hula, kafafen yaɗa labarai da masu zaɓe domin tabbatar da gudanar da zaɓe cikin lumana da mutunta tsarin dimokuraɗiyya.
