Wajibi ne ga yan Arewa su zaɓi Tinubu a 2027 – Alhassan Doguwa
Wajibi ne ga yan Arewa su zaɓi Tinubu a 2027 - Alhassan Doguwa
Ɗan majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana cewa al’ummar Arewa na da nauyin ɗabi’a na mara wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu baya domin ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027, tare da tabbatar da nasarar sauran ’yan takarar jam’iyyar APC.
Doguwa ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa, inda ya yi kira ga al’ummar Arewa da su haɗa kai wajen zaɓen Tinubu domin ci gaba da zaman lafiya da zaman tare a Najeriya.
Ya kuma bayyana cewa goyon bayan da yake samu daga jama’a na yau da kullum na nuna cewa har yanzu akwai masu mara wa Tinubu da APC baya a yankin Arewa, duk da abin da ya kira farfagandar da ake yi wa jam’iyyar.
Sanarwar tasa na zuwa ne yayin da jam’iyyun siyasa ke ƙara shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen shekarar 2027, inda APC ke ƙoƙarin ƙarfafa goyon bayanta a yankunan ƙasar, musamman Arewa, domin sake zaɓen Tinubu a wa’adi na biyu.
