UBEC ta kaddamar da shirin tallafin Dala Miliyan 552 domin inganta Ilimin yara Miliyan 29
ta kaddamar da shirin tallafin Dala Miliyan 552 domin inganta Ilimin yara Miliyan 29
Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Ƙasa (UBEC) ta ce shirin tallafin dala miliyan 552.18 daga Bankin Duniya na shirin inganta ilimin yara miliyan 29 a faɗin Najeriya.
Shirin mai suna HOPE-EDU zai kuma shafi malamai 500,000, makarantun gwamnati 65,000 da cibiyoyin koyar da ilimin manya da sauran waɗanda ba sa cikin tsarin makarantu na yau da kullum guda 10,000.
Sakatariyar zartarwa ta UBEC, Dakta Aisha Garba, ce ta bayyana hakan yayin wani taron kwanaki biyu da shugabannin hukumomin ilimin bai ɗaya na jihohi (SUBEB) suka gudanar a Abuja, domin tattauna shirye-shiryen aiwatar da shirin.
Ta ce an kuma tsara gina sabbin azuzuwa 13,000 domin faɗaɗa damar samun ilimi da inganta koyarwa da karatu a ƙasar.
Aisha, ta bayyana cewa shirin zai mayar da hankali kan inganta ƙwarewar malamai, samar da kayan koyarwa, bunƙasa karatu da rubutu da lissafi, tare da ƙara damar samun ilimi ga yaran da ba sa zuwa makaranta, musamman waɗanda ke yankunan karkara da iyalai masu ƙaramin ƙarfi.
Ta ƙara da cewa za a raba kuɗaɗen shirin bisa sakamakon ayyukan da aka cimma da kuma cika ƙa’idojin da aka amince da su.
Sai dai shugabar UBEC ta yi gargaɗin cewa nasarar shirin za ta dogara ne da yadda gwamnatocin jihohi za su nuna ƙwazo wajen aiwatar da shi, tare da ware kuɗaɗen da ake buƙata a kasafin kuɗinsu.
Ta buƙaci shugabannin SUBEB su sanar da gwamnatocinsu game da shirin tare da neman goyon bayansu, musamman wajen samar da kasafin kuɗin shekarar 2027, domin tabbatar da cewa an cimma manufofin shirin.
