Tinubu ya zargi ’yan adawa da haddasa matsalolin yunwa da talauci a Najeriya

0
Tinubu ya zargi ’yan adawa da haddasa matsalolin yunwa da talauci a Najeriya

Tinubu ya zargi ’yan adawa da haddasa matsalolin yunwa da talauci a Najeriya

Spread the love

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya zargi ’yan adawa da haddasa matsalolin yunwa da talauci da ke addabar al’ummar ƙasar, yana mai cewa gwamnatinsa na ƙoƙarin kawo ƙarshen waɗannan ƙalubale.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, yayin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a filin wasa na Ranchers Bees, wanda aka fi sani da Kaduna Township Stadium, a jihar Kaduna, gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Tinubu ya ce masu adawa da gwamnatinsa na yawan sukar ta kan matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa, amma a cewarsa, su ne suka haifar da yunwa da talaucin da ake fuskanta.

Shugaban ya bayyana cewa gwamnatinsa na ƙoƙarin shawo kan matsalolin, inda ya ce: “Ina jin abokan hamayyata suna magana kan yunwa da talauci. Wa ya haddasa su? Su ne suka haddasa yunwa da talauci, mu kuma muna ƙoƙarin kawar da su.”

Haka kuma, shugaban ya kare salon tafiyar da gwamnatinsa, inda ya ce ana biyan albashin ma’aikata a kan lokaci, tare da yabawa gwamnonin APC bisa abin da ya bayyana a matsayin ƙoƙarinsu na bunƙasa jihohinsu.

Ya kuma gode wa al’ummar jihar Kaduna bisa goyon bayan da suka ba shi a zaɓen shekarar 2023, yana mai neman su sake ba shi dama domin ci gaba da aiwatar da manufofinsa na ci gaba da bunƙasa tattalin arziki.

Tinubu ya kuma buƙaci ’yan Najeriya da su sake zaɓensa a shekarar 2027, yana mai alƙawarin kawo wadata, ci gaba da farfaɗo da tattalin arziki.

Ya bayyana ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen a Kaduna a matsayin wani mataki na fara neman goyon bayan masu kaɗa ƙuri’a domin samun wa’adi na biyu.

Sai dai matsin tattalin arziki da tsadar kayan masarufi na daga cikin manyan batutuwan da ake tafka muhawara a kansu yayin da ƙasar ke shirin tunkarar zaɓen mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *