Atiku ga Tinubu: “Zargin ’yan adawa da haddasa yunwa kauce wa gaskiya ne Alhali kai ne ke riƙe da Mulki”
Atiku ga Tinubu: “Zargin ’yan adawa da haddasa yunwa kauce wa gaskiya ne Alhali kai ne ke riƙe da Mulki”
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya soki Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan zargin ’yan adawa da haddasa yunwa da talauci a ƙasar, yana mai cewa hakan wata hanya ce ta kauce wa alhakin da ke kan gwamnatinsa.
Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), ya bayyana hakan ne bayan Tinubu ya zargi ’yan adawarsa da haddasa matsalolin yunwa da talauci yayin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a Kaduna ranar Asabar.
A cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na ADC, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce zargin ’yan adawa da haddasa yunwa bayan jam’iyyar APC ta shafe kusan shekaru 11 tana mulkin tarayya, ya nuna mantuwa da tarihin siyasar ƙasar ko kuma ƙoƙarin kauce wa gaskiya.
Ya jaddada cewa ’yan Najeriya na da cikakken ’yancin tambayar gwamnati dalilin tsadar rayuwa, ƙaruwar talauci da sauran matsalolin da suke fuskanta a kullum.
Atiku ya kuma buƙaci Tinubu ya yi wa ’yan Najeriya bayani kan tasirin cire tallafin man fetur da faduwar darajar naira, tare da bayyana yadda aka kashe kuɗaɗen gwamnati a wasu fannoni.
Haka kuma, ya yi tambayoyi kan kashe kuɗaɗe a ƙarƙashin shirin tabbatar da tsaron makamashi, kuɗaɗen ayyukan bututun mai na kamfanin NNPC da kuma wasu kuɗaɗen da ya ce suna buƙatar cikakken bayani.
Ya kuma soki yadda aka ƙaddamar da aikin babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna daga cikin filin wasa, yana mai cewa jawabi ko bikin yanke kintinkiri ba ya tabbatar da kammala aiki.
A ƙarshe, Atiku ya ce bai kamata gwamnatin Tinubu ta yi amfani da zargin ’yan adawa wajen kauce wa tambayoyin da jama’a ke yi kan halin da tattalin arzikin ƙasar yake ciki ba.
Ya kuma yi gargaɗin cewa zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 zai zama wata dama da ’yan Najeriya za su tantance ayyukan gwamnatin APC bisa abin da suka gani da kuma irin rayuwar da suke ciki.
A cewarsa, abin da jama’a suke buƙata shi ne amsoshi da matakan magance matsalolin da suke addabar ƙasar, ba wai a riƙa ɗora wa wasu laifin da ya shafi shugabanci ba.
