Tinubu ya yi murna da kuɗin sufuri ya ragu da Naira 1,000 a Abuja

0
Spread the love

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana farin cikinsa kan rahotannin raguwar kuɗin sufuri a wasu sassan Abuja, sakamakon amfani da motocin da ke aiki da iskar gas da aka matse (CNG).

Shugaban ya ce zuba jari da gwamnatinsa ke yi a motocin CNG da na lantarki na taimakawa wajen rage wa ’yan Najeriya kuɗin zirga-zirga a daidai lokacin da farashin man fetur ke ƙaruwa.

Tinubu ya bayyana cewa wani fasinja da ke tafiya daga Masaka zuwa Berger a Babban Birnin Tarayya, Abuja, yanzu yana biyan naira 500 maimakon naira 1,500 da yake biya a baya.

Hakan na nufin fasinjan yana samun rangwamen naira 1,000 a kowace tafiya, abin da shugaban ya ce zai taimaka wajen rage nauyin tsadar rayuwa ga al’umma.

Shugaban ya kuma kawo misalin wasu fasinjoji da ke tafiya daga Enugu zuwa Nsukka, inda ya ce kuɗin tafiyar ya ragu daga naira 4,000 zuwa naira 1,600, wanda ke ba su damar adana naira 2,400 a kowace tafiya.

Ya danganta wannan sauyi da shirin gwamnati na faɗaɗa amfani da motocin CNG da na lantarki domin samar da sufuri mai sauƙin araha.

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta ci gaba da faɗaɗa shirin sufuri mai amfani da CNG tare da haɗin gwiwar jihohi, domin rage kuɗin sufuri da tasirin tashin farashin man fetur ga ’yan Najeriya.

Sai dai rahotannin raguwar farashin sun shafi wasu hanyoyi da aka ambata, kuma ba lallai ba ne dukkan fasinjoji a Abuja da sauran jihohi su fara cin gajiyar wannan rangwame a lokaci guda.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *