Tattalin Arzikin Najeriya na farfaɗowa, yayin da hauhawar farashi kuma na raguwa – Oluremi Tinubu
Sake zaɓen Tinubu zai kawo wa ’yan Najeriya wadata - Remi Tinubu
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, ta bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya na samun sauƙi a hankali, tana mai cewa ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje na ƙaruwa, yayin da hauhawar farashin kayayyaki ke raguwa.
Ta bayyana hakan ne a Abuja yayin wani taron wayar da kan mata da ƙarfafa musu gwiwa da kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC ya shirya.
Oluremi Tinubu ta ce wasu daga cikin sauye-sauyen manufofin tattalin arziki da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar sun fara haifar da sakamako.
Ta lissafa ƙarin sha’awar masu zuba jari, tallafawa manoma da kuma shirin rancen kuɗin karatu ga ɗaliban jami’o’i a matsayin wasu daga cikin matakan da gwamnatin ta ɗauka.
Uwargidan shugaban ƙasar ta kuma yi kira ga mata da su ci gaba da goyon bayan gwamnatin APC, tana mai cewa matakan da Shugaba Tinubu ya ɗauka sun zama wajibi domin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar.
Ta ce ya kamata mata su taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan al’umma game da manufofin gwamnati da irin tasirinsu.
A nata ɓangaren, matan da ke Majalisar Wakilai sun yi alƙawarin samo ƙuri’u 20,000 daga kowace mazabar tarayya domin sake zaɓen Shugaba Tinubu a 2027.
Hajiya Fatima Tajudeen Abbas, matar Kakakin Majalisar Wakilai, ta ce matan za su koma mazabunsu domin gudanar da kamfen gida-gida da wayar da kan jama’a, musamman mata, kan buƙatar mara wa Tinubu baya a zaɓen 2027.
