Sake zaɓen Tinubu zai kawo wa ’yan Najeriya wadata – Remi Tinubu
Sake zaɓen Tinubu zai kawo wa ’yan Najeriya wadata - Remi Tinubu
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai kawo wa ’yan Najeriya ƙarin wadata da ci gaba idan aka sake zaɓensa a karo na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Ta bayyana hakan ne a wani gangamin siyasa da aka gudanar a Lafia, babban birnin Jihar Nasarawa, domin neman goyon bayan sake zaɓen Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima.
Oluremi ta ce saƙon ranar ’yancin kai da Shugaban Ƙasar ya gabatar a ranar 1 ga Oktoba, mai taken “Daga Sauye-sauyen Tattalin Arziki zuwa Wadata”, ya nuna cewa gwamnati na ƙoƙarin sauya matsin da aka fuskanta sakamakon gyare-gyaren tattalin arziki zuwa ci gaba da wadata.
Ta kuma yi ikirarin cewa tattalin arzikin ƙasar na samun daidaito, yayin da darajar canjin kuɗi ke inganta kuma masu zuba jari ke dawowa Najeriya.
Uwargidan Shugaban Ƙasar ta kuma bayyana cewa gwamnati na ƙoƙarin magance matsalar ƙarancin abinci, musamman ga yara, mata masu juna biyu da masu shayarwa, ta hanyar shirye-shiryen tallafin abinci.
Ta ƙara da cewa ɗalibai ma na amfana da shirye-shiryen tallafa wa harkokin ilimi, tare da yaba wa gwamnonin jihohi kan ayyukan raya ababen more rayuwa da suke gudanarwa.
Ta yi kira ga ’yan jam’iyyar APC da magoya bayanta da su kai saƙon manufofin gwamnati zuwa ga al’umma a jihohinsu, tare da neman goyon bayan masu zaɓe domin tabbatar da nasarar Tinubu da Shettima a 2027.
Ta ce sake zaɓen shugabannin zai taimaka wajen gina tattalin arziki mai ƙarfi, samar da al’umma mafi aminci da kuma samar da Najeriya mai ci gaba.
