Na cire tallafin man fetur ne domin ceto Najeriya daga durƙushewar tattalin arziki – Tinubu
Bafarawa ya kafa wa Tinubu Sharaɗin samun zaman lafiya kafin ya samu kuri’unsa a 2027
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa cire tallafin man fetur da ya yi a ranar farko ta hawansa mulki a watan Mayun 2023 ya zama wajibi domin hana ƙasar faɗawa cikin matsanancin halin kuɗi da ka iya jefa ta cikin fatara.
Shugaban ya ce a wancan lokacin gwamnati ba ta da isassun kuɗaɗen da za ta ci gaba da biyan tallafin man fetur.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, yayin wani taro da ƙungiyar City Boy Movement ta shirya a Abuja, inda ya sake jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta dawo da tsarin tallafin man fetur na baya ba.
Ya ce ci gaba da biyan tallafin zai ƙara jefa kuɗaɗen gwamnati cikin matsin lamba, tare da hana aiwatar da wasu muhimman ayyukan ci gaba.
Shugaban ya kuma soki ’yan siyasar da ke alƙawarin dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe su, yana mai cewa hakan tamkar komawa baya ne bayan an riga an ɗauki matakin gyara tattalin arzikin ƙasar.
Ya yi amfani da kwatanci daga addini, inda ya bayyana cewa ba za a nemi Annabi Musa ya koma Masar ba bayan ya bar ta, yana mai nuni da cewa bai kamata Najeriya ta koma tsarin da ta yi watsi da shi ba.
Tinubu ya jaddada cewa duk da wahalhalun da cire tallafin ya janyo wa ’yan Najeriya, gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki da ta fara.
Sai dai matakin cire tallafin ya ci gaba da zama babban batu a muhawarar siyasa da tattalin arziki a ƙasar, musamman ganin yadda tsadar man fetur ta shafi farashin kayayyaki da tsadar rayuwar al’umma.
