Masu kaɗa kuri’a miliyan 103 ne za su yanke hukunci tsakanin Tinubu, Atiku, Obi da sauran ’yan takara a 2027 – INEC
Masu kaɗa kuri’a miliyan 103 ne za su yanke hukunci tsakanin Tinubu, Atiku, Obi da sauran ’yan takara a 2027 – INEC
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa adadin masu rajistar zaɓe a Najeriya ya haura miliyan 103, waɗanda za su samu damar kaɗa ƙuri’a a babban zaɓen ƙasar na 2027.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana hakan yayin wani taro da aka gudanar a Abuja.
Amupitan ya ce adadin ya ƙaru ne bayan kammala matakai uku na aikin Ci gaba da Rajistar Masu Zaɓe (CVR), inda aka samu sabbin masu rajista 10,772,421. Ya ce an kuma kammala tantance bayanan masu rajistar ta hanyar tsarin Automated Biometric Identification System (ABIS), lamarin da ya kai adadin masu zaɓe na ƙasar sama da miliyan 103.
INEC ta kuma bayyana cewa za a fara rabon katunan PVC ga masu zaɓe a faɗin ƙasar daga 9 ga Oktoba, 2026, yayin da hukumar ta ce ta ɗauki matakai na ƙarfafa tsarin fasahar zaɓe, ciki har da sayen sabbin na’urorin BVAS guda 57,000, domin ƙara tabbatar da sahihancin zaɓen 2027.
Zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Ƙasa an tsara gudanar da shi ne a 16 ga Janairu, 2027, inda manyan ’yan takara irin su Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar da Peter Obi, da sauran ’yan takara 18 da INEC ta amince da su, za su fafata domin samun damar jagorantar Najeriya.
