Majalisar Sarkin Musulmi za ta kafa Bankin Musulunci domin yaƙi da talauci da samar da ayyukan yi
Sarkin Musulmi ya buƙaci Tinubu da ’yan siyasa su guji abin da zai haddasa rikici lokacin zaɓe
Majalisar Sarkin Musulmi ta bayyana shirin kafa bankin ƙananan kuɗaɗen lamuni na Musulunci mai suna Caliphate Islamic Microfinance Bank, domin yaƙi da talauci, samar da ayyukan yi da inganta rayuwar al’umma a Najeriya da yankin Afirka ta Yamma.
Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya bayyana hakan ne yayin buɗe wani taron horaswa na kwanaki uku kan tsarin Baitul Mal wat Tamweel (BMT), wanda Bankin Raya Musulunci tare da Hukumar Zakka da Wakafi ta Jihar Sakkwato suka shirya.
Ya ce bankin zai taimaka wa ƙananan ’yan kasuwa wajen samun kuɗaɗen gudanar da kasuwancinsu, faɗaɗa ayyukansu da samar da guraben aikin yi.
Ya ƙara da cewa shirin ya kai wani mataki na ci gaba, inda wasu masu zuba jari, ciki har da na ƙasashen waje, suka nuna sha’awar haɗa kai wajen aiwatar da shi.
Ya bayyana fatan bankin zai zama abin koyi ga Najeriya da sauran ƙasashen Afirka ta Yamma wajen bunƙasa tattalin arziki bisa tsarin kuɗaɗen da suka dace da koyarwar Musulunci.
A nasa jawabin, shugaban Hukumar Zakka da Wakafi ta Jihar Sakkwato, Lawal Maidoki, ya jaddada cewa bai kamata a dogara da tallafin zakka da sadaka kaɗai wajen rage talauci ba.
Ya ce wajibi ne a haɗa tallafin da damar bunƙasa sana’o’i, samar da jarin kasuwanci da horas da masu ƙaramin ƙarfi domin su dogara da kansu, su inganta rayuwarsu, kuma a nan gaba su ma su iya taimaka wa sauran mabukata.
