INEC za ta sake fitar da jerin sunayen ’yan takara na zaɓen 2027 bayan nazari kan masu korafi
INEC za ta sake fitar da sunayen ’yan takarar zaɓen 2027 bayan bitar korafe-korafe
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) ta sanar da shirin fitar da sabon jerin sunayen ’yan takarar zaɓen 2027 bayan kammala bitar korafe-korafen da ta karɓa daga ’yan takara da jam’iyyun siyasa.
Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana hakan a Gombe yayin ganawarsa da manema labarai.
Ya ce hukumar na nazarin korafe-korafe da suka shafi kuskuren rubuta sunayen ’yan takara da kuma wasu matsaloli da suka taso yayin tantance waɗanda jam’iyyun siyasa suka tsayar takara.
Ya ƙara da cewa hukumar ta ware wa kanta wa’adin kwanaki 14 domin gudanar da bitar.
Matakin na zuwa ne bayan wasu ’yan takara da jam’iyyun siyasa sun nuna rashin gamsuwa da jerin sunayen da INEC ta fitar a baya, inda wasu suka nemi a sake duba matsayinsu bisa ƙa’idojin doka da hukuncin kotuna.
Sai dai hukumar ba ta bayyana takamaiman ranar da za ta fitar da sabon jerin sunayen ba. Ana sa ran matakin zai fayyace matsayar INEC kan korafe-korafen da aka gabatar yayin da shirye-shiryen babban zaɓen 2027 ke ci gaba.
